A ran 21 ga wata, zaunannen wakilin kasar Sin a hukumar MDD da ke birnin Geneva, Sha Zukang ya bayyana cewa, shawarwarin siyasa hanya ce kadai da ta kamata a bi don neman daidaita matsalar Darfur da kyautata halin jin kai da ake ciki a shiyyar Darfur.
A gun taron MDD kan hakkin dan Adam na karo na 61 da aka yi a ran nan, an yi shawarwari a kan 'kudurin hakkin dan Adam na Sudan', inda kuma aka zartas da shi. Yayin da Sha Zukang ya yi bayani a kan kudurin, ya ce, ya kamata a bi ra'ayin kyautata halin jin kai da ake ciki a shiyyar da maido da kwanciyar hankali da bunkasuwar tattalin arziki da kuma neman sulhu tsakanin kabilu don daidaita matsalar Darfur.

|