Ran 21 ga wata, jami'in kungiyar kiyaye zaman lafiyar kasar Cote d'Ivoire ta MDD ya tabbata cewa, sojojin gwamnatin kasar da dakaru masu yin adawa da gwamnatin sun riga sun fara janye manyan makamai daga fagen daga.
Bisa labarin da muka samu, aikin janye makamai zai shafi kwanaki hudu, kuma sojojin kayaye zaman lafiya na MDD da sojojin kasar Faransa suna dudduba aikin. Jimi'in ya ce, abin da sojojin suke yi zai saukaka halin da ake ciki a Cot d'Ivoire. [Musa]
|