Ran 18 ga wata, a birnin Harare, fadar mulkin kasar Zimbabwe, mutane da yawa suka taru domin bikin ranar cikun shekaru 25 da aka samu 'yancin kan kasar.
Robert Gabriel Mugabe, shugaban kasar Zimbabwe ya yi jawabi a wurin biki, inda ya yi bitar fafutukar da jama'ar kasar suka yi domin neman samun 'yancin kan kasa, da kuma nasarorin da suka samu bayan samun mulkin kan kasa. Ya ce, bunkasa tattalin arziki shi ne babban nauyin da ke kan wuyan gwamnatin kasar. Domin yaki da takunkumin da kasashen yamma suka sanya wa kasar Zimbabwe, gwamnatin kasar za ta ci gaba da yalwata huldar da ke tsakaninta da kasashen Asiya da na Afirka, yadda za a raya tattalin arzikin kasar.
Ban da wannan kuma, Kennrth David Kaunda, tsohon shugaban kasar Zambia, wanda ya hallara a wurin bikin bisa gayyatar da aka yi masa, ya gaya wa maneman labaru cewa, kada a dogara a kan sauran mutane yayin da ake neman bunkasuwar nahiyar Afirka. Ya kamata, 'yan Afirka su hada kansu yadda za su raya nahiyarsu. (Bello)
|