Ran 18 ga wata, a kasar Zimbabwe, an yi bikin ranar cikun shekaru 25 da kasar ta sami 'yancin kai, inda shugaba Mugabe na kasar ya yi kira ga jama'arsa da su hada kansu domin raya kasa.
Ya ce, ana bukatar hadin kai ba ma kawai a lokacin da ake fafutukar neman 'yancin kan kasa ba, hatta ma a yayin da ake yaki da duhun kai da talauci da yunwa da kuma cututtuka.
Ban da wannan kuma, ya nuna cewa, idan ba tare da taimako da goyon baya da sauran kasashen Afirka suka bayar ba, kasar Zimbabwe ba zata samu 'yancin kan kasa ba. Jama'ar kasar Zimbabwe ba za su manta da wannan ba. (Bello)
|