Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-18 10:53:13    
Kasashe daban daban na Afirka suna daukar matakai don fuskantar da cutar Marburg

cri

Bisa labarin da muka samu daga kafofin watsa labarai na kasar Cameroon a ran 17 ga watan nan, an ce, kasashe daban daban na Afirka suna daukar matakai iri daban daban domin shawo kan yaduwar cutar Marburg.

A ran 16 ga watan, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Zimbabwe ta riga ta yi wa tashoshin shigi da fici da asibitoci gargadi kan cutar Marburg, inda ta bukaci a yi bincike ga mutane masu shiga kasar daga Angola.

Ban da wannan kuma, gwamnatin Zambia ta riga ta yi wa jihohi uku na kasar da suke makwabtaka da Angola gargadi kan cutar Marburg, kuma an riga an dauki kayayyakin likitoci da kuma yi furofaganda da yawa a jihohin nan.

Bugu da kari kuma, kasashen Kenya da Afirka ta Kudu da Kango Brazzaville da Kango Kinshasa da kuma Cameroon sun yi gargadi da kuma dauki matakai don shawo kan yaduwar cutar Marburg.(Kande Gao)