Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-16 16:58:43    
Robert Zoellick ya kai ziyara a kudancin kasar Sudan

cri
A ran 15 ga wata, mataimakin sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka Mr. Robert Zoellick ya kai ziyara a kudancin kasar Sudan, inda ya yi shawarwari da John Garang, shugaban kungiyar 'yantattar da jama'ar Sudan, wato tsohuwar kungiyar mafi girma a kudancin kasar Sudan da ke adawa da gwamnati.

A gun shawarwarin, Mr. Garang ya bayyana wa Mr. Zoellick shirin da kungiyarsa ta tsara domin makomar kasar Sudan, da shirin yin amfani da kudaden da aka dauki alkawarin cewa za a samar wa kasar Sudan a gun babban taron samar wa kasar Sudan da aka yi kwanan baya. Mr. Garang ya kuma jadadda cewa, kungiyar 'yantattar da jama'ar Sudan za ta yi kokarinta wajen kawo karshen hargitsin da ke kasancewa a shiyyar Darfur. Mr. Zoellick ya kuma nemi gwamnatin Sudan da kungiyar 'yantattar da jama'ar Sudan da su gaggauta saurin tafiyar da yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a tsakanin kudu da arewa da aka kulla a watan Janairu na shekarar nan. (Sanusi Chen)