A ran 15 ga wata, an isar da wasu kayayyakin likitanci a birnin Luanda, babban birnin kasar Angola. Kasar Sin ne ta samar wa kasar Angola wadannan kayayyakin likitoci domin yin fama da ciwon zazzabin ha'bo na cutar Marburg. Yanzu an riga an mika wa gwamnatin Angola wadannan kayayyakin likitanci.
Wadannan kayayyakin likitanci da suka kai kudin Sin yuan miliyan 1 suna kunshe da safar hannu na likitanci da tufafin likitanci da abubuwan rufe fuska da takalmomin likitanci da dai makamatansu. Za a isar da dukkansu a birnin Luanda cikin sau 3 kafin karshen watan nan.
A gun bikin mikawa, mataimakin mininstan kiwon lafiya Jose Van-Dunem ya wakilci gwamnatin Angola ya gode da sahihin taimakon da abutar da kasar Sin ta samar mata. Mr. Ding Shan, wani babban jami'in ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Angola ya bayyana cewa, ko shakka babu gwamnati da jama'ar kasar Angola za su ci nasara wajen kawar da ciwon zazzabin ha'bo na cutar Marburg. (Sanusi Chen)
|