|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-04-16 16:22:49
|
Wakilin tsofaffin dakaru masu adawa da gwamnatin Cote d'Ivoire sun sake koma gwamnatin sulhuntar al'umma
cri
A ran 15 ga wata, wakilai 2 na tsofaffin dakarun masu adawa da gwamnatin Cote d'Ivoire, wato kungiyar sabon karfi ta kasar sun sake koma gwamnatin sulhuntar al'umma ta kasar.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, ministan wasannin motsa jiki da ministan yankunan kasa sun halarci taron ministoci da gwamnatin kasar Cote d'Ivoire suka yi a wannan rana. Wannan ne karo na farko da wakilan kungiyar sabon karfi ta kasar Cote d'Ivoire suka koma gwamnatin bayan kungiyar ta shelanta cewa ta janye jikinta daga gwamnatin sulhunta al'umma a karshen shekarar bara. (Sanusi Chen)

|
|
|