|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-04-15 13:15:14
|
Kamata ya yi kasashen Afirka su sami zaunannun kujeru 2 na kwamitin sulhu na M.D.D., in ji Mr. Mbeki
cri
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Thabo Mbeki ya bayyana a birnin Capetown, hedkwatar kasar Afirka ta Kudu a ran 14 ga watan nan cewa, kamata ya yi kasashen Afirka su sami zaunannun kujeru guda 2 na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ta haka kasashen Afirka za su kara taka rawarsu a cikin al'amuran kasa da kasa.
Mr. Mbeki ya ambaci yin gyare-gyare kan Majalisar Dinkin Duniya a cikin jawabin da ya yi a majalisar dokokin kasar a ran nan. Ya yi nuni cewa, ya kamata kasashen Afirka su sami kujerun din din din guda 2 a cikin kwamitin sulhu, haka kuma suna da ikon kin amincewa, wannan ya taka muhimmiyar rawa wajen aikin awar da talauci a duniya da majalisar take yi.(Tasallah)
|
|
|