A ran 14 ga wata a kan shafin Internet na kungiyar WHO, an bayar da wata sanarwa, inda ta yi wa wadanda za su je kasar Angola kashedin cewa, dole ne su dauki matakan yin rigakafi domin hana kamuwa da annobar ciwon zazzabin ha'bo na cutar Marburg.
Wannan ne karo na farko da kungiyar WHO ta bayar da irin wannan kashedi bayan bullowar annobar ciwon zazzabin ha'bo na cutar Marburg a kasar Angola tun watan Oktoba na shekarar bara. Sanawar ta bayyana cewa, ya kamata wadanda suka shiga kasar Angola su kara mai da hankulansu kan irin wannan cuta da kuma magance yin cudanya da masu kamu da ciwon. A cikin sanarwar, an kuma ba da shawara cewa, wadanda ba su da lafiya sosai kada su je kasar Angola, musamman ma lardin Uige, inda annobar ciwon cutar zazzabin ha'bo na cutar Marburg ya fi tsanani.
Gwamnatin kasar Zambiya ita ma ta yi kashedi kan annobar ciwon zazzabin ha'bo na cutar Marburg a lardunanta guda 3 masu makwabtaka da kasar Angola a ran nan.(Tasallah)
|