|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-04-15 10:19:08
|
 |
Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka ya kalubalanci gwamnatin Sudan da ta warware matsalar Darfur
cri
Mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka Robert Zoellick da ke ziyara a kasar Sudan ya kalubalanci gwamnatin kasar Sudan da ta warware matsalar yankin Darfur a birnin Khartoum, hedkwatar kasar a ran 14 ga wannan wata. Ya kuma jaddada cewa, kasarsa ba za ta cika alkawarin da ta yi na ba da taimakon kudi da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 1.7 ba , illa gwamnatin Sudan ta warware matsalar Darfur.
Mr. Zoellick ya yi shawarwari da mataimakin shugaba na farko na kasar Ali Osman Mohammed Taha da ministan harkokin wajen kasar Mustata Ismail Osman da kuma wakilan kungiyar 'yantar da jama'ar kasar Sudan da ke taka muhimmiyar rawa a kudancin kasar daya bayan daya. Mr. Zoellick ya yi wa kafofin yada labaru bayani cewa, ya yaba wa gwmanatin kasar Sudan da kungiyar 'yantar da jama'ar kasar Sudan saboda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a farkon wannan shekara, ya kamata kasashen duniya su goyi bayan kokarin da Kawancen Kasashen Afirka ya yi don warware matsalar Darfur.(Tasallah)
|
|
|