A ran 14 ga wata, yayin da ministan kiwon lafiya na kasar Zambia Brian Chituwo yake amsa tambayoyin da kafofin watsa labaru suka yi masa, ya ce, gwamnatin kasar ta riga ta bayar da gargadi na cutar Marburg ga johohi 3 na kasar da ke iyakar kasa da ke tsakaninta da kasar Angola tare da daukan matakai domin hana cutar ta yadu zuwa kasar Zambia.
Mr Chituwo ya ce, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ta riga ta bayar da wajibabbun na'urorin asibiti ga jihohin 3 da ya ambata tun farko, kuma tana shirin koyar wa jama'ar wurin ilmin da abin ya shafa. Ban da wannan kuma, kasar Zambia tana yin mu'amala da kungiyar kiwon lafiya ta duniya, ta yadda za ta iya samun labarun da abin ya shafa game da cutar.(Danladi)
|