Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-14 21:32:59    
Hu Jintao da Olusegun Obasanjo sun yi shawarwari a nan Beijing

cri

A ran 14 ga wata da yamma, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo wanda ke yin ziyara a nan kasar Sin, inda bangarorin biyu suka yi musanyar ra'ayoyinsu kan dangantakar da ke tsakanin kasashen nan biyu da sauran matsalolin kasa da kasa da na yankuna da ke jawo hankulansu tare.

Da farko da hannu biyu ne, Hu Jintao ya wakilci gwamnati da jama'ar kasar Sin yana maraba da zuwan Olusegun Obasanjo, a matsayin shugaban kasar Nijeriya da shugaban wannan zagaye na kawancen kasashen Afirka. Mr. Hu ya yi imani cewa, ziyarar da Mr. Obasanjo ke yi a nan kasar Sin dole ne za ta kara ingiza yin musanye-musanye da hadin guiwa a fannoni daban-daban a tsakanin kasashen biyu, kuma za ta kara ci gaban dangantakar hadin guiwa irin ta sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasar Nijeriya. Bugu da kari, tabbas ne za ta karfafa abutar gargajiya da ke kasancewa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, kuma za ta ba da taimako ga bunkasuwar sabuwar dangantakar abuta a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a nan gaba.

Kafin a yi shawarwari, Hu Jintao ya yi gagarumin bikin maraba da zuwan Olusegun Obasanjo. Bayan sun yi shawarwari, shugabannin nan biyu za su halarci bikin sa hannu a kan wasu takardun hadin guiwar kasashen nan biyu.

A ran 14 ga wata da safe ne shugaba Olusegun Obasanjo na kasar Nijeriya ya iso nan birnin Beijing domin fara yin ziyararsa ta aiki ta kwanaki 4 a nan kasar Sin bisa gayyatar da Hu Jintao ya yi masa. Wannan kuma karo na 3 ne da shugaba Obasanjo ya kawo wa kasar Sin ziyara bayan ya hau kan mukamin shugaban kasar Nijeriya a shekarar 1999. (Sanusi Chen)