Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-14 11:23:56    
Kasar Mozambique da kasar Angola za su mayar da hadin gwiwar da ke tsakaninsu

cri

Ran 13 ga wata, a birnin Luanda, fadar mulkin kasar Angola, shugaba Dos Santos na kasar da takwaransa na kasar Mozambique, Armando Guebuza, wanda ke ziyara a kasar Angola, sun yi zantawa da juna, inda bangarorin 2 suka nuna cewa, za su mayar da hadin gwiwar da ke tsakaninsu wanda aka daina shi a da sabo da yakin basasa.

Mista Dos Santos ya yi nuni da cewa, sabo da kasashen 2 na kama da juna wajen tarihi da gargajiya da kuma addini, kasar Angola tana daukan hadin gwiwar da ke tsakaninta da kasar Mozambique da muhimmanci. Ziyarar da Mista Guebuza ya kai wa kasar Angola dama ce ga kasashen 2, wadda za a yi amfani da ita domin sake kulla dangantakar hadin gwiwa yadda za a amfana wa jama'ar kasashen 2.

Mista Guebuza ya jaddada cewa, makasudin ziyararsa shi ne, domin nuna niyyar da gwamnatin kasar Mozambique ta dauka wajen karfafa hadin kan kasashen 2, kuma zai yi tattaunawa da shugaba Dos Santos kan hanyar da za a bi domin karfafa hadin gwiwar kasashen 2. (Bello)