Bisa labarin da muka samo daga kasar Tanzania, an ce, a ran 13 ga wata, a Dar es Salaam, babban birnin kasar Tanzania, ministan tsaron kasa ta kasar Sin Cao Gangchuang wanda ke yin ziyara a kasar Tanzania ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar, Philemon Sarungi.
A gun shawarwari, Mr.Cao ya daranjanta zumuncin gargajiya da kuma huldar hadin gwiwa tsakanin Sin da Tanzania cikin dogon lokaci, ya kuma gode wa bangaren Tanzania sabo da goyon bayan da ya baiwa kasar Sin a kan "kasar Sin daya tak a duniya" da aikin neman dinkuwar kasar Sin da hakkin dan Adam da dai sauransu. Ya ci gaba da cewa, kasar Sin tana son karfafa huldar aminci da hadin gwiwa tsakanin sojojin kasashen biyu a sabon halin da ake ciki.
A nasa bangaren kuma, Mr.Sarungi ya nuna godiya ga kasar Sin sabo da taimako da goyon bayan da ta baiwa kasar Tanzania shekara da shekaru. Ya jaddada cewa, Tanzania za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka a kan goyon bayan "manufar kasar Sin daya tak a duniya" da "dokar hana ballewa daga kasa".(Lubabatu Lei)
|