A ran 13 ga wata, a birnin Jakarta, ministan harkokin waje na kasar Indonesia Hasan Wirayuda ya shelanta cewa, a kalla dai shugabannin kasashen Asiya da na Afirka 56 za su halarci taron Asiya da Afirka na karo na biyu wanda za a yi a birnin Jakarta daga ran 22 zuwa ran 23 ga watan nan da muke ciki, inda kuma za su tattauna maganar hadin gwiwa tsakanin nahiyoyin biyu a fannoni da dama.
A gun taron watsa labaru da aka shirya a ran nan, Mr.Wirayuda ya ce, mai yiwuwa ne za a kara samun mahalartan taron a kusantowarsa.
An ce, a gun taron nan na Asiya da Afirka, za a bayar da sanarwa da kuma tsarin ka'adojin aiki angane da kulla huldar aminci tsakanin Asiya da Afirka. Ban da wannan, a ran 24 ga wata, a birnin Bandung, za a yi bikin murnar cikon shekaru 50 da aka kira taron Asiya da Afirka na karo na farko, wato taron Bandung.(Lubabatu Lei)
|