Robert Mugabe, shugaban kasar Zimbabwe ya yi nuni da cewa, gwamnatin kasar tana gamsuwa da dangantakar aminci da ke tsakaninta da kasashen Asiya, kuma za ta dauki matakai domin ci gaba da karfafa huldar da ke tsakaninta da kasar Sin da kasar Malaysia da kasar Singapore, da dai sauran kasashen Asiya.
Shugaba Mugabe ya yi wannan bayani ne a ran 13 ga wata, lokacin da yake karbar jiragen saman horo na K-8 da kasar Sin ta gabatarwa kasar Zimbabwe.(Bello)
|