Ran 12 ga wata, kakakin tawagar MDD da ke kasar Kongo Kinshasa ya gaya wa maneman labaru cewa, sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD za su kammala aikinsu na kwance damarar dakaru farar hula na yankin Ituri da ke arewa maso gabashin kasar Kongo Kinshasa kafin karshen watan Yuni.
Kakakin ya nuna cewa, tare da tallafin da tawagar musamman ta MDD ta bayar, gwamnatin kasar Kongo Kinsha ta kaddamar da shiri mai taken 'kwance damara da koma ciki al'umma' a yankin Ituri a watan Satumba na bara, wannan ya sa yawancin dakaru farar hula su ajiye damararsu. Yanzu, a yankin Ituri, sai dai dakaru 2500 kawai ba su ajiye makamansu ba tukuna.
Da ma, tawagar MDD ta taba yin gargadin cewa, sojojin kiyaye zaman lafiya za su kai farmaki ga dakaru farar hula wadanda suka ki ba da kansu. (Bello)
|