Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ba da sanarwar shugaba a ran 12 ga watan nan, inda ya yi maraba da kungiyar adawa da gwamantin kasar Ruwanda ta FDLR saboda ta yi alkawarin daina yin amfani da makamai, ya kuma yi kira ga dakaru masu adawa da gwamnati da su mika wa kungiyar musamman ta Majalisar Dinkin Duniya dukan makamansu nan da nan.
Sanarwar ta bayyana cewa, kwamitin sulhu yana ganin cewa, matakin da kungiyar FDLR ta dauka ya gabatar da wata muhimmiyar dama ga maido da zaman lafiya a kasar Congo(Kinshasa) da samun sulhuntawar al'umma a kasar Ruwanda da kuma komar da huldar da ke tsakanin kasashen nan 2 yadda ya kamata. Kwamitin sulhu ya yi kira ga dakarun da ke adawa da gwamantin Ruwanda da su mika wa kungiyar musamman ta majalisar da ke kasar Congo(Kinshasa) dukan makamansu nan da nan, da aiwatar da shirin 'kwance damara da yin ritaye daga aikin soja da koma su gida daga kasar Congo(Kinshasa) da sake shiga cikin zaman al'umma', ban da wannan kuma, su ba da taimako ga kotun manyan laifuffuka ta duniya kan matsalar kasar Ruwanda da ya kanmala aikinsa.(Tasallah)
|