Sababbin 'yan majalisar dokokin kasar Zimbabwe 150 sun yi rantsuwar kama aiki a birnin Harare, hedkwatar kasar a ran 12 ga watan nan, sa'an nan kuma, sun zabi shugaban jam'iyyar ZANU-PF da ke rike da mulkin kasar John Nkomo da ya zama sabon shugaban majalisar dokokin kasar.
Lokacin da ya ke jawabi bayan da ya zama sabon shugaban majalisar dokokin kasar, Mr. Nkomo ya yi kira ga jam'iyya mai rike da mulkin kasar da kuma jam'iyyun adawa da su kawar da sabanin da ke tsakaninsu da kuma kiyaye moriyar kasarsu tare. Ya kara da cewa, a cikin wa'adin aikinsa na shekaru 5 masu zuwa, dukan 'yan majalisar dokokin kasar ta karo ta 6 suna dauke da nauyin da ke bisa wuyansu na ba da tabbacin cewa, za su warware dukan matsalolin da kasar ke fuskanta, tare da yin la'akari da moriyar dukan mutanen kasar Zimbabwe.(Tasallah)
|