
A gun taron maneman labaru da kungiyar kiwon lafiya ta WHO ta yi a ran 12 ga wata a birnin Geneva, Fadela Chaib, mai magana da yawun kungiyar ta yi nuni da cewa, kungiyar tana damuwa sosai kan cewar, har yanzu gwamnatin kasar Angola ba ta kebe wasu mutanen da ake tsammanin cewa sun kamu da cutar Marburg ba.
Madam Chaib ta ce, a kasar Angola, an bar wasu mutanen da ake tsammanin cewa sun kamu da cutar Marburg a gidajensu, ba a kebe su a cikin asibiti domin binciken lafiyar jikinsu ba. Wannan zai haddasa kara yaduwar annoba a tsakanin al'umma, domin wadannan mutane ka iya yada cutar wa danginsu. (Bello)
|