 A gun taro na 4 na ministocin kawancen kasashen Afrika da kawancen kasashen Turai da aka yi a ran 11 ga watan nan, Oluyemi Adeniji na Nigeria, kasar da ke shugabancin wannan karo ta kawancen kasashen Afrika kuma ministan harkokin waje na kasar Nigeria ya karfafa cewa, a gyare gyaren hukumomin MDD da za a yi ya kamata kasashen Afrika su samu kujeru 2 na zaunannun kasashen kwamitin sulhu. A yayin da MDD ke gyare gyare, ya kamata ta yi la'akari da maganar zaman lafiya da maganar raya kasa gaba daya. Wannan bayanin da Adeniji ya yi ya shaida burin kasashen Afrika na neman halartar harkokin kasashen duniya da neman samun ci gaba a wajen raya kasa. Yanzu sai ku saurari wani sharhin da mai yin sharha na gidan rediyon kasar Sin ya yi, kanun sharhin nan shi ne
A yayin da MDD ke gyare gyare ya kamata ta yi la'akari da bukatun kasashen Afrika sosai.
Babban yankin Afrika yana da dadadden tarihi, kuma daya ne daga cikin mafarin wayin kai na 'yan Adam. yanzu akwai kasashe 53 a Afrika. A shekarun baya kasashen Afrika da yawa sun raba kansu daga mulkin mallaka, sun samu 'yancin kan al'umma, sabo da haka suna kishin samun damar shiga cikin harkokin kasashen duniya, kuma su kara ba da gudummuwarsu a fagen siyasa na duniya. Amma a cikin zaunannun kasashen kwamitin sulhu na MDD, ko kasar Afrika guda daya ma babu. Sabo da haka bayan da aka fitar da shirin gyara MDD. Sai aka kulla yarjejeniya a gun taron ministoci da aka yi a watan Febrairu na bana, inda aka tsai da cewa, za a yi kokarin neman samun kujeru biyu na zaunannun kasashen kwamitin sulhu na MDD, ta yadda kasashen Afrika za su kara ba da amfaninsu a cikin harkokin duniya. Wannan bukatun da kasashen Afrika suka gabatar ya samu goyon baya daga wajen kasashe da yawa, ciki har da kasar Sin. Liu Jianchao, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya nuna cewa, da ba zama mai dorewa da arziki na Afrika, da ba zaman lafiya da ci gaba na duniya. Kasar Sin tana nuna goyon baya ga kasashen Afrika da su kara ba da amfani a hukumomin MDD, ciki har da kwamitin sulhu.
Tattalin arziki na duniyar yanzu yana bunkasuwa da saurin gaske, ratar da ke tsakanin kasashe masu sukuni da kasashe masu tasowa tana kara habaka. Sabo da haka maganar raya kasa ita ce maganar da ta fi muhimmanci ga kasashen Afrika. Amma har yanzu akwai matsaloli da yawa a gaban kasashen Afrika. Sabo da haka idan kasashen Afrika suna son samun ci gaba mai dorewa, dole ne a yayin da kasashen Afrika ke yin kokarinsu ya kamata kasashe masu sukuni na yammacin duniya su ba da hakikanin taimako. Amma a shekarun baya an yi sabbin sauye sauye a kasashen duniya, wato maganar zaman lafiya ta fi jawo hankulan kasashen yammacin duniya. Har wasu kasashe masu sukuni suna nufin cewa, sai a yi gyare gyare duk bisa maganar zaman lafiya. Cikin halin haka ne ministan harkokin waje na kasar Nigeria ya yi kira ga MDD da ta yi gyare gyare hade da maganar raya kasa. Wannan ya shaida matsayin kawancen kasashen Afrika, kuma ya shaida burin kasashe masu tasowa.(Dogonyaro)
|