Ran 11 ga wannan wata gwamnatin kasar Cote d'Ivoire ta musanta sanarwar da tsohon dakarun adawa da gwamnati (wato the New Forces) na yanzu ya bayar, kan wai askarawan sojojin gwamnatin kasar za su kai masa hari.
Wani mashawarci kan harkokin tsaron kasar na shugaban kasar Cote d'Ivoire ya bayyana a ran nan cewa, sanarwar da dakarun New Forces ya bayar a ran 10 ga watan nan, wai cewa rundunar sojin gwamnatin kasar tana daukar sojojin haya da kuma yin shirin kai masa hari, ko kusa ba shi da kan gado. A sa'i daya kuma ya yi suka kan dakarun New Forces saboda sun nemi cin amanar yarjejeniyar zaman lafiya da bangarori daban daban na kasar Cote d'Ivoire suka rattaba hannu a kai a birnin Pretoria a kwanan baya.(Tasallah)
|