Bisa sabuwar sanarwar da ma'aiktar kiwon lafiya ta Angola da kungiyar kiwon lafiya ta duniya, wato WHO suka bayar a ran 11 ga wata, an ce, a kasar Agola, yawan mutanen da suka kamu da cutar Marburg ya karu har zuwa 221, kuma 203 daga cikinsu sun riga mu gidan gaskiya.
An ce, a halin yanzu, an gano masu cutar Marburg da suka mutu a larduna 6 daga cikin larduna 18 na kasar Angola. Kuma a lardin Uige da ke arewacin kasar, wato asalin wurin da cutar ta bullo, yawan mutanen da suka mutu sabo da cutar Marburg ya kai 184. Lardin nan ya zama lardin da aka fi samun mutanen da suka mutu sabo da cutar.
A nata bangaren kuma, ma'aikatar kiwon lafiya ta Angola ta bayyana cewa, yanzu an riga an kafa tashoshin bincike a muhimman hanyoyin na lardin Uige, haka kuma an kafa cibiyoyin bincike a dukan lardunan da aka tarar da cutar.(Lubabatu Lei)
|