A ran 11 ga wata, a birnin Addis Ababa, kungiyar samar da ci gaba tsakanin gwamnatocin kasashen gabashin Afirka, wato IGAD ta shelanta cewa, za ta ba da jagoranci wajen kafa wata zaunanniyar rudunar sojojin kiyaye zaman lafiya a gabashin Afirka, don tinkarar rikicin da mai yiwuwa ne za a samu a shiyyar.
Sakataren zartaswa na IGAD Affalla Hamad Bashir ya ce, za a kafa hedkwatar rundunar nan a birnin Addis Ababa, kuma rundunar za ta kasance mai kunshe da mutane 5,500.
Mr.Bashir ya ci gaba da cewa, mai yiwuwa ne za a gama kafa rundunar kafin watan Yuni na shekarar 2006, kuma tana wani kashi ne daga cikin zaunanniyar rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta Afirka da kawancen kasashen Afirka ke yin shirin kafawa. Kwamitin sulhu na kawancen kasashen Afirka ne zai yi mata jagoranci.(Lubabatu Lei)
|