A ran 10 ga wata a birnin Nairobi, an gama gasar cin kofin kulob na kungiyoyin mata na kwallon raga na kasashen Afirka, inda wata kungiyar mata ta kwallon raga ta kulob din ta Kenya ta zama zakara. Wannan ne karo na 9 da kungiyar nan ta kasar Kenya ta ci wannan gasa a cikin tarihin gasar.
Bayan gasar, mai horarwa na kungiyar kwallon raga ta Kenya Mr. Daviz ya ce, a cikin tarihi, kasar Kenya kasa ce da take da karfin gasar kwallon raga ta mata a Afirka. Kungiyar mata ta kwallon raga ta kasar Kenya ta taba wakiltar sauran kasashen Afirka ta halarci wasanin motsa jiki na Olympic da aka yi a birnin Sydney da a birnin Athens. Ban da wannan, kungiyoyin mata na kwallon raga na kasar Kenya sun taba zama zakara har sau 14 a gun gasannin kwallon raga ta mata ta Afirka. (Sanusi Chen)
|