Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-11 10:57:26    
Kasashen Afirka sun yi kira da a gaggauta bunkasa aikin ba da ilmi

cri
Bisa labarin da muka samo dagan kasar Algeria, an ce, a ran 10 ga wata, an yi taron ministocin ba da ilmi na kasashen gamayyar Afirka na karo na biyu a kasar Algeria, inda mahalartan taron sun jaddada muhimmancin aikin ba da ilmi a kan farfado da Afirka, kuma sun yi kira da a kara saurin bunkasa aikin ba da ilmi.

Shugaban kasar Algeria Abdelaziz Bouteflika da shugaban kwamitin kawancen kasashen Afirka Alpha Ouamar Konare da kuma babban daraktan kungiyar kula da harkokin kimiyya da ilmi da al'adu ta MDD, wato UNESCO, Koichiro Matsuura sun halarci bikin bude taron. A cikin jawabinsa, Mr.Bouteflika ya bayyana cewa, ya kamata kasashen Afirka su dora matukar muhimmanci a kan aikin ba da ilmi, su kara mu'amala da hadin gwiwa da juna, ta yadda za su tinkari kalubalen da bunkasuwar kasashen duniya bai daya ke kawowa.

A taron da za a shafe kwanaki biyu ana yinsa, mahalartan taron za su tattauna da kuma zartas da tsarin fayiloli dangane da inganta aikin ba da ilmi a kasashen Afirka, kuma za su yi musanyar ra'ayoyi a kan amfanin aikin ba da ilmi da na al'adu wajen farfado da Afirka.(Lubabatu Lei)