Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-11 10:45:58    
An dakatar da yin taron shugabannin kasashe 6 na Afirka kan matsalar Darfur ta Sudan

cri
Ministan harkokin wajen kasar Masar Ahmed Abul Gheit ya ba da sanarwa a birnin Alkahira, hedkwatar kasar a ran 10 ga watan nan cewa, an dakatar da yin taron shugabannin kasashe 6 na Afirka kan matsalar yankin Darfur na kasar Sudan, wanda aka tsai da kudurin yinsa a birnin Sharm- Sheikh na kasar Masar a ran 20 ga watan nan.

A gun taron ganawa da manema labaru da aka yi a ran nan, Mr. Gheit ya bayyana cewa, an dakatar da yin taron shugabannin kasashe 6 na Afirka kan matsalar yankin Darfur na kasar Sudan, don biyan bukatun wasu kasashe masu halartar taron. Ya kara da cewa, za a tsai da lokacin yin wannan taro ta hanyar yin shawarwari tsakanin kasashe masu halartar taron.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, a gun taron shugabannin da za a yi, shugabannin kasashe 6 na Afirka wato kasashen Sudan da Masar da Libya da Nijeriya da Chadi da kuma Gabon za su yi tattaunawa kan hanyoyin hana kara lalacewar matsalar yankin Darfur, sa'an nan kuma za su nemi wata dabarar da bangarorin daban daban na kasar Sudan suke amincewa da ita don warware matsalar Darfur, a karkashin tsare-tsaren Kawancen Kasashen Afirka.(Tasallah)