Ran 7 ga wata, a cibiyar Cairo babban birnin kasar Masar an yi wani al'amarin fashewar bomb, mutane 4 sun mutu, kuma 16 suka ji rauni, wasu da ke cikinsu masu yawoshakatawa na kasashen waje.
Ma'aikatar harkokin gida ta bayyana cewa, al'amarin fashewar baomb ta faru a wata kasuwar kusa da Masallacin al-Azhar. Fashewar ta kashe mutane 4, a ciki har da wani dan Amurka da wani dan Faransa, kuma akwai mutane 16 suka ji rauni, wasu da ke cikinsu 'yan kasashen waje ne.
Bayan al'amarin ya faru, 'yan sanda sun toshe wurin, ministan harkokin gida da na kiyaye zaman lafiya sun je wurin don shugabantar aikin ba da agaji da kuma bincike al'amarin.
|