Ran 7 ga wata, kwamitin babban zabe na kasar Zimbabwe ya bayyana cewa, ba a yi tafka maduga ba a babban zabe da aka yi a ran 31 ga watan Maris.
George Chiweshe shugaban kwamitin babban zabe na kasar ya ce, an yi babban zabe ta hanyar aminci da kuma a gaban fili, yawan kuriu da gwamnati ta kididdiga babu kuskure.
Chiweshe ya ce, har zuwa ran 6 ga wata, kwamitin babban zabe bai karbi ko wane iri zargi a rubuce ba. yana ganin cewa, wasu jam'iyyu sun zargi an yi tafka maduga a babban zabe ta hanyar matsakaici wannan maras dacewa. [Musa]
|