
A ran 5 ga wata, lokacin da yake ganawa da babban jami'i mai gabatar da kara na kotun babban laifi ta duniya, babban sakatare Kofi Annan na M.D.D. ya gabata masa wata takardar sunayen masu laifuffuka wadanda ake yi musu tuhumar cewa suna da laifuffukan yaki da kuma take hakkin bil Adam a cikin rikicin da ke kasancewa a shiyyar Darfur ta kasar Sudan.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, kwamiti mai 'yancin kai na M.D.D ne ya gabatar wa Kofin Annan wannan takarda bayan ya dudduba halin mutumtaka da ake ciki a shiyyar Darfur a watan Fabrairu na shekarar nan. Wannan kwamiti ya kuma gabatar wa kotun babban laifi ta Duniya wasu takardu game da wadanda ake yi musu tuhumar yin laifuffuka a Darfur. (Sanusi Chen)
|