Kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Fred Eckhard ya ba da sanarwa a ran 4 ga wannan wata cewa, Mr. Kofi Annan ya mai da hankalinsa kan zaben 'yan majalisar dokoki da aka yi a kasar Zimbabwe a kwanan baya.
Sanawar nan ta bayyana cewa, Mr. Annan ya lura da cewa, an yi zaben 'yan majalisar dokokin kasar Zimbabwe a cikin halin zaman lafiya, ba a samun lamarin nuna karfin tuwo ba. A sa'i daya kuma, Mr. Annan ya mai da hankali kan bayanin da jam'iyyar adawa da gwamnatin Zimbabwe ta yi, wato ba ta samu adalci a lokacin zaben 'yan majalisar dokokin kasar ba. Mr. Annan yana ganin cewa, ba za a shimfida kwanciyar hankali da hadin gwiwa da kuma farfado da tattalin arziki a kasar Zimbabwe ba, illa za a kasance amincewar juna a kasar, gwamnatin kasar Zimbabwe tana da nauyin samar da irin wannan amincewar juna. Sa'an nan kuma, Mr. Annan yana fata bangarorin kasar Zimbabwe za su iya yin tattaunawa mai amfani a tsakaninsu.(Tasallah)
|