Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-05 10:01:23    
An kori ministar gine-gine ta kasar Nijeriya daga mukaminta

cri
A ran 4 ga wata, shugaba Olusegun Obasanjo na kasar Nijeriya ya sa hannu a kan wani umurni, inda ya kori Mobolaji Osomo, ministar gine-gine da raya biranen kasar Nijeriya daga mukaminta domin tuhumar da aka yi mata na karban rashawa da al'amubazzaranci.

A wannan rana, gwamnatin kasar Nijeriya ta bayar da wata sanarwa, inda ta ce, gwamnatin Nijeriya za ta binciki yadda madam Osomo ta sayar wa wasu manyan jami'an kasar gidaje masu inganci, amma farashinsu yana karkashin na kasuwa, kuma za ta hori wadanda suke da dangantaka da matsalar.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, lokacin da take kan mukamin ministar gine-gine da raya biranen kasar Nijeriya, madam Osomo ta samar wa wasu manyan jami'an gwamnati da wasu 'yan majalisar dokokin kasar wasu gidaje masu inganci fiye da dari 2, amma farashin wadannan gidaje yana karkashin na kasuwa. (Sanusi Chen)