 Bisa labarin da wakilan gidan Rediyo Kasar Sin suka aiko mana, an ce, Madam Phumzile Mlambo-Ngcuka, shugabar kungiyar 'yan kallo ta kawancen raya kudancin Afrika ta bayyana a ran 3 ga wata cewa, a ganin kungiyarta, zaben majalisar dokoki da aka yi a kasar Zimbabwe a ran 31 ga watan jiya ya bayyana burin jama'ar kasar.
Madam Ngcuka ta kuma bayyana a wannan rana cewa, da yake ba a sami ingantattun shaidu ba, kungiyar 'yan kallon ba ta iya gaskanta ra'ayi da jam'iyyun hamayya ta gabatar dangane da magudin zabe da aka yi a wasu wurare ba.
A ranar da hukumar zabe ta bayar da sakamakon zabe, Mugabe, shugaban kasar Zimbabwe ya yi kira ga jam'iyyun hamayya da ta amince da sakamakon zabe, kuma ya bayyana cewa, kungiyar Zanu-PF ta yi shirin hadin guiwarta da jam'iyyun hamayya a cikin majalisar dokokin kasar. daga duk fannoni. (Halilu)
|