A ran 31 ga wata, babban sakataren MDD Kofi Annan ya bayar da wata sanarwa, inda ya nuna maraba ga dakarun da ba su ga maciji da gwamnatin Ruwanda, wato dakarun 'yantar da Ruwanda, da su yi shelar kwance damara bisa son ransu.
A cikin sanarwar, an kuma sa kaimi ga gwamnatocin kasashen Congo Kinshasa da Ruwanda da su dauki mataikai kamar yadda ya kamata, don tabbatar da komawar dakarun nan a Ruwanda lami lafiya. Ban da wannan, an kuma nemi dakarun musamman na MDD a kasar Congo Kinshasa da su ba da taimako.
A ran nan kuma, a birnin Rome na Italiya, dakarun 'yantar da Ruwanda sun bayar da sanarwar cewa, suna son gama yakin da suke yi da gwamnatin Ruwanda, su kwance damara, kuma su koma Ruwanda.(Lubabatu Lei)
|