A ran 31 ga watan Maris, kwamitin harkokin zabe mai zaman kansa na kasar Afirka ta Tsakiya ya bayyana cewa, a gun babban zaben shugaban kasar da aka yi a ran 13 ga watan Maris, cikin 'yan takarar zabe 11, babu wanda yawan kuri'un da ya samu ya zarce rabin adadin kuri'u, 'yan takara biyu wadanda suka sami kuri'u masu rinjaye wato shugaban kasar mai ci Francois Bozize da tsohon firayin ministan kasar Martin Ziguele za su shiga babban zabe na karo na biyu da za a gudanar a ran 1 ga watan Mayu na bana.
Bisa sakamakon kididdigar da kwamitin ya yi, an ce, Mr Bozize ya sami kuri'un da yawansu ya kai kashi 42.97 bisa dari yayin da Mr Ziguele ya sami kuri'un da yawansu ya kai kashi 23.53 bisa dari.
Kwamitin ya ci gaba da cewa, a 'yan kwanaki masu zuwa za a bayyana sakamakon zaben majalisar kasa wanda ake yinsa a yayin da ake gudanar da babban zaben shugaban kasar.(Danladi)
|