Labarin da aka kawo mana ya bayyana cewa,a ran 30 ga watan nan da muke ciki, a kasar Angola,an rufe taron shawarwari neman hadin guiwar tattalin arziki da ciniki na tsakanin kasar Sin da kasashe masu yaren Portugal.
Wata sanarwar da aka bayar bayan taron nan ta bayyana cewa, wannan taron shawarwari ya sa 'yan kasuwa mahalartan taro sun kara fahimtar kyakyawan muhallin bunkasuwar tattalin arziki na sauran kasashe da damar yin ciniki da tsarin zuba jari.Wannan sanarwa ta kuma bayyana cewa, irin taron shawarwari da musaye musaye da yin hadin guiwa zai iya ingiza cudanyar tattalin arziki da ciniki tsakanin kasar Sin da kasar Portugal da kyau. Kuma ya kamata za a shirya irin taro a lokaci lokaci.
Ministan masana'anta na birnin Angola ya bayyana cewa, yana fatan kasashe daban daban za su kara yin aikatayya tare da kasar Portugal a kan sassa daban daban.(Dije)
|