A ran 30 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri mai lambar 1592, don tsawaita wa'adin aikin dakarun musamman na MDD da ke kasar Congo Kinshasa da rabin shekara, wato zuwa ran 1 ga watan Oktoba, shekarar 2005.
A sa'i daya kuma, kudurin ya nemi gwamnatocin Uganda da Ruwanda da Congo Kinshasa da dai sauransu da su dauki matakai don hana haramtacciyar zirga-zirgar makamai a yankunansu, ya kuma jaddada cewa, dakarun musamman suna da ikon daukar ko wane irin mataki don kiyaye lafiyar takalawa da kuma dukiyarsu.
Ban da wannan, kudurin ya kuma nemi rukunoni daban daban na gwamnatin wucin gadi na Congo Kinshasa da su yi kokarin daukar matakai don samar da sharudda masu kyau wajen tsara tsarin dokoki da gudanar da zabe ta hanyar dimokuraddiya a kasar tun da wuri.(Lubabatu Lei)
|