Shugaba Mugabe na kasar Zimbabwe ya yi nuni da cewa, tabban ne, Jam'iyyar Hadin Al'umma da Kaunar Kasa ta Afirka ta ZANU-PF wadda ke rike da ragamar mulki a kasar za ta ci nasara a wajen zaben 'yan majalisar dokoki da za a yi a ran 31 ga wata. Har wa yau kuma, ya yi kira ga kasashen duniya da su martaba zabin da jama'ar kasar Zinbabwe za su yi.
Ran 30 ga wata, a garin Glen Norah da ke kudu maso yammacin lardin Harare, Jam'iyyar ZANU-PF ta yi taro na karshe kafin zaben da za a yi, inda shugaba Mugabe ya yi wannan bayani. Ya ce, idan jam'iyyar ZANU-PF ta ci zaben, to, kamata ya yi, wanda ya fadi a takarar ya nuna girmamawa ga sakamakon zaben, bai kamata ba ya matsa wa mai cin zabe lamba tare da goyon bayan da kasashen waje suka bayar. (Bello)
|