Bisa labarin da aka samu a ran 29 ga watan nan an ce, an kama 'yan sanda 15 na kasar Sudan domin an yi musu tuhumar karkashe mutane da yin wasoso a Darfur, kuma za a tura keyarsu zuwa kotu don yanke musu hukunci.
Yassin, ministan shari'a na kasar Sudan ya ce, wannan mafari ne kawai, a albarkacin wannan aiki ne ma'aikaatar shari'a ta Sudan tana son shaida cewa, tana da karfin yanke hukunci ga masu barkata laifi. (Dogonyaro)
|