Ministan ma'aikatar kula da harkokin bauta wa al'umma da kwadago da jin dadin jama'ar kasar Zimbabwe Paul Mangwana ya bayyana a birnin Harare, hedkwatar kasar a ran 28 ga watan nan cewa, labarin da kafofin yada labaru na kasar Birtaniya suka bayar, wato wai gwamnatin kasar Zimbabwe ta ki ba da taimakon abinci ga masu goyon bayan jam'iyyar adawa da gwamantin wadanda suke zaune a lardin Matebeleland ta arewa da na Matebeleland ta kudu karya ne kawai.
Mr. Mangwana ya kara da cewa, tun daga watan Nuwamba na shekarar bara har zuwa yanzu, yawan abinci da gwamnatin kasarsa ta bayar ga lardin Matebeleland ta arewa da na Matebeleland ta kudu da kuma lardin Bulawayo ya fi yawan da suka bukata sosai. Ya kuma ci gaba da cewa, gwamnatin kasarsa ta riga ta ba da abinci kyauta ga tsofaffi da masu fama da talauci da nakasasu na larduna guda 10 na kasar.(Tasallah)
|