A ran 28 ga wata, kakakin ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Angola Carlos Alberto ya bayyana cewa, annobar cutar Marburg wadda aka samu a yankunan arewa na kasar a watan Oktoba na bara ta riga ta haddasa mutuwar mutane 126.
Mr Alberto ya ci gaba da cewa, wata yarinya wadda shekarunta ba su kai biyu ba ta rasa rayuwarta a sakamakon cutar a jihar Uige da ke arewacin kasar a ran 27 ga wata da dare, wannan kuma ya sa yawan mutanen kasar da suka mutu a sakamakon cutar ya karu har ya kai 122.
Sabo da karancin ma'aikatar asibiti, kasar Angola ta riga ta nemi taimako daga kasa da kasa domin shawo kan mumunar cutar.(Danladi)
|