Ran 28 ga wata, an fara aikin rajistar masu jefa kuri'a a duk fadin kasar Togo domin shara fagen babban zaben da za a yi a kasar.
Bisa labarin da kwamitin zabe mai zaman kansa na kasar Togo ya bayar, an yi hasashen cewa, za a yi rajistar masu jefa kuri'a fiye da miliyan 2 kafin babban zabe. Kuma aikin rajista zai kai tsawon kwanaki 8 ana yi.
Za a yi babban zaben kasar Togo ne a ran 24 ga wata mai zuwa. Yanzu an samu masu takara 4, cikinsu sun hada da Faure Gnassingbe, dan tsohon shugaba Eyadema, wanda ya samu goyon baya daga Kawancen Jama'ar kasar Togo, jam'iyyar da ke kan karagar mulki, da Emmanuel Bob Akitani, mataimakin shugaban jam'iyyar Kawancen Karfin Canja Hali, wanda kawancen 'yan hamayya ke ba shi kwarin gwiwa. Ana zaton cewa, za a samu kazamin takara a tsakanin Mista Faure da Mista Akitani wajen babban zaben da za a yi. (Bello)
|