Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-29 16:59:09    
An samu labarin yaduwar annobar cutar kwalara a babban birnin kasar Senegal

cri
Bisa labarin da kofofin watsa labaru na kasar Senegal suka bayar, an ce, bayan da aka samu nasarar shawo kan yaduwar annobar cutar kwalara na 'yan makonni, an kuma sake samun yaduwar annobar cutar a birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal, a halin yanzu da akwai mutane 7 wadanda suka kamu da cutar sun je asibitoci da ke kusa da su.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ta bayyana cewa, sassan da abin ya shafa na gwamnatin suna mai da hankali sosai a kan halin da ake ciki na yaduwar cutar tare da daukan matakan da suka wajaba ciki har da kashe kwayoyin cuta a wuraren tattara ruwa da wasu wuraren jama'a. Haka kuma ma'aikatar ta yi kira ga dukkan jama'ar kasar da su yi rigakafin da magance annobar cutar kwalara da warkar da cutar cikin hadin gwiwa, kuma su kula da kiwon lafiyar kansu da na jama'a, idan wani ya yi zawo ko ciwon ciki ko amai ko zazzabi, dole ne ya je asibiti nan da nan domin ganin likita.(Danladi)