A ran 27 ga watan nan , an gama gasanni guda 10 na sharan fagen wasan cin kofin duniya a kasar Jamus a shekarar 2006. A filin wasan kwallon kafa na kasar Mali a Afrika an yi tashin hankali har an katse gasar kafin karshen lokacin gasar.
A kungiya ta daya, a cikin gasar tsakanin Kungiyar Mali da Kungiyar Togo masu sha'awar kwallon kafa na kasar Mali sun yi tashin hankali a minti na 90 a lokacin da kungiyar Togo ta ci maki 2 da 1 kan Kungiyar Mali . Tashin hankalin ya katse gasar . Idan Kungiyar wasan kwallon kafa ta Afrika ta tsai da kudurin cewa, Kungiyar Togo ta ci nasara , to , kungiyar Senegal da ta Zambia da ta Togo sun ci maki 13 kuma sun kai matsayi na farko .
A kungiya ta 2 ,Kungiyar Congo (Kinshasa) ta yi kunnen doki da Kungiya Ghana . Wato sun ci maki daya da daya.
A kungiya ta 3 , Kungiyar Kameroon ta ci maki 2 da 1 kan Kungiyar Sudan .Kungiyar Kwat Dibuwa ta ci maki 3 da ba ko daya kan Kungiyar Benin.
A kungiya ta 4 , Kungiyar Zimbabwe ta ci maki 2 da ba ko daya kan Kungiyar Angola . A wannan kungiyar , Nijeriya ta ci maki 13 wato ta kai matsayi na farko yanzu . ( Ado)
|