
Nas tana binciken ciwon Marburg
Ran 24 ga wata, jami'in ma'aikatar harkokin kiwon lafiya ya tabbata cewa, Ciwon Marburg da aka samu daga watan Oktoba na shekarar 2004 da ke arewacin kasar ya riga ya kashe mutane 98, a ciki akwai nas 5.
Jimi'i Filomena Wilson wanda ya kiyaye halin ciwon Marburg ya ce, ran 22 a asibitin lardin Uige nas biyu sun mutu don gamu da ciwon Marburg.
Bisa labarin da muka samu, kungiyar gammayr Turai za ta ba da kudin Turai dubu 500 don taimako Angola ta yaki da Ciwon.[Musa]
|