
A ran 24 ga wata,ranar shawo kan cutar fuka ta duniya,kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta bayar da wani rahoto na shekara ta 2005 kan shawo kan cutar fuka a duniya.Rahoton nan ya ce cutar fuka a Afrika ta fi damu mutane,yawan mutane masu kamuwa da cutar kanjamau da cutar fuka ta kame su da kuma yawansu da suka mutu dukkansu sun fi jawo hankulan mutane.
Rahoton nan ya ce tun daga shekara ta 1990,daga bangarorin shida suka fi samun yaduwar cutar fuka a duniya,bangarorin biyar da yawan mutanen da suka kama cutar fuka ya ragu sannu a hankali,Afrika tana waje da su.Har wa yau dai mutanen da cutar fuka suka kame su suna karuwa a halin yanzu.
|