Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-23 18:04:13    
Kawancen Kasashen Afirka zai kafa zaunannun sojojin kiyaye zaman lafiya

cri
Jami'in musamman na kula da zaman lafiya da tsaron kai na Kawancen Kasashen Afirka Said Djinnit ya bayyana a ran 23 ga watan nan cewa, kawancen nan ya yi shirin kafa zaunannun sojojin kiyaye zaman lafiya masu yawan mutane dubu 15, don warware hargitsin wadanda mai yiwuwa ne za su faru a nahiyar Afirka.

Bayan da aka kammala taron shawarwari tsakanin Kawancen Kasashen Afirka da kungiyar tattalin arziki ta Afirka, Mr. Djinnit ya bayyana wa kafofin yada labaru cewa, wannan zaunannen sojin kiyaye zaman lafiya zai kunshi birged guda 5 da kuma sojoji daga kasahsen Afirka, an kiyasta cewa, za a kafa shi kafin karshen watan Yuni na shekarar 2006.

Mr. Djinnit ya kara da cewa, a farkon kafuwarsa, sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya za su yi masa jagora, kuma za su kiyaye zaman lafiya tare. Amma idan lokaci ya yi, wannan zaunannen sojin Afirka zai kiyaye zaman lafiya da kansa.(Tasallah)