A ran 22 ga wata a birnin Luanda, wani jami'in ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Angola ya amince da cewa, ya zuwa yanzu, a arewacin kasar, mutane 96 sun mutu domin sun kamu da ciwon ha'bo. Wannan jami'i ya kara da cewa, cutar Marburg ce ta jawo ciwon ha'bo a kasar.
A wannan rana, jami'in ma'aikatar harkokin waje ta kasar Angola ya shelanta cewa, bayan da cibiyar kayyade ciwace-ciwace ta Atlanta ta kasar Amurka ta yi nazari kan misali da aka dauka daga gawar mutanen da suka mutu domin kamuwa da ciwon, cibiyar ta tabbatar da cewa, cutar Marburg ce ta jawo ciwon.
A watan Oktoba na shekarar bara, a karo na farko ne ciwon ha'bo ya bullo a lardin Uige da ke arewacin kasar Angola. Yawancin mutanen da suka kamu da ciwon yara ne da ba su kai shekaru 5 da haihuwa ba. (Sanusi Chen)
|