Ran 22 ga wata, wasu 'yan sintiri na sojojin gwamnatin Kongo Kinshasa sun gamu da farmakin da 'yan yakin sunkurun kabila suka yi, wani ya mutu, kuma saura biyu ba a sami su ba.
An kai farmakin ne a yankin Kafi inda aka kai farmaki ga sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Bangladesh a ran 25 ga watan Febrairu. Har yanzu, cikin dakarun kabilu shida na yankin Iruri babu wani ya dauki nauyin al'amarin.
Yankin Kafi yana gabar tebkin Albert, watan kungiyar 'yan yakin sunkurun suna sarrafa da wurin. Don amsa bukatar kungiyar wakilan MDD gwamnatin ta kama shugaban wannan kungiyar 'yan yakin sunkurun a farkon watan nan.[Musa]
|